Mata masu juna biyu zasu rika ansar kudi domin zuwa awo

Mata masu juna biyu zasu rika ansar kudi domin zuwa awo

- Ya zuwa yanzu, asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya dauki nauyin wani shirin lafiya da nufin rage mace macen mata masu juna biyu da kananan yara a jihohin arewacin Najeriya goma

- Jihohin da suka hada da Bauchi, Kano, Jigawa, Adamawa, Borno, Nassarawa, Plateau Taraba, Yobe da kuma Gombe

Mata masu juna biyu zasu rika ansar kudi domin zuwa awo

A wani sabon yunkuri na magance matsalar mace macen mata yayin haihuwa uwar gidan gwamnan jihar Adamawa Hajiya Maryam Bindo tare da hadin gwiwar asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya,UNICEF, sun kaddamar da shirin bada tukwuicin kudi ga matan dake zuwa awo a jihar.

Alkalumman hukumomin kiwon lafiya na nuni da cewa mata da dama ne ke mutuwa da kuma jariran da suka haiwa sakamakon rashin zuwa awo yayin da suke da juna biyu .

KU KARANTA: Rundunar sojojin Najeriya ta kama sojan gona

Bincike dai na nuni da cewa, kimanin mata dari biyar daga cikin dubu dari ke mutuwa lokacin haihuwa a kudancin Najeriya,yayin da kuma kimanin dubu daya da dari biyu ke mutuwa daga cikin dubu goma lokacin haihuwa a arewacin Najeriya wato baya ga karuwan adadin matan da ke fama da matsalar yoyon futsari ta dalilin matsalar haihuwan.

Kuma don magance wannan matsalar nema yasa uwar gidan gwamnan jihar Adamawa, Hajiya Maryam Bindo tare da hadin gwiwar ofishin asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF daukan nauyin wannan sabon shirin lafiya da nufin rage mace macen mata masu juna biyu da kananan yara a jihar Adamawa.

Da take kaddamar da wannan shiri a kauyen Malabu dake karamar hukumar Fufore, uwar gidan gwamnan jihar Adamawa,Hajiya Maryam Bindo , tace bullo da shirin ya zama wajibi domin magance matsalar mace macen matan yayin haihuwa.

Shiko jami’in asusun tallafawa yaran – UNICEF, Dr Abdulai Kaikai,yace dole ne a tashi tsaye wajen magance wannan matsala na mace macen mata da jarirai yayin haihuwa.

‘’Wannan matsalar tana ciwa hukumomi tuwo a kwarya,kuma dole mu tashi tsaye,don haka a madadin UNICEF,muna jinjinawa jihar Adamawa bisa kaddamar da wannan shiri da aka yi,’’ inji shi.

Tun farko a jawabin ta sakatariyar ma’aikatar mata a jihar Maisaratu Bello cewa ta yi: ‘’Mata ya kamata mu gane duk abun da gwamnati ke yi domin mu mata ne domin mune ginshikin iyali. Gidan da ba mace, ba gidan mune komi. To yau rana ce dake da muhimmanci na kaddamar da wannan shiri da matar gwamnan mu ta kaddamar.’’

Shima Dr Abdullahi Belel, shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar Adamawan ya shawarci mata da su yi rajista,domin amfana da shirin inda ma yace:

‘’A yau kowace mace da take da juna biyu in ta yi rajista da shirin za’a bata N1500 to amma sai ta yi rajista. Sannan kuma duk zuwan da tayi na awo bayan rajista za’a bata N500,duk zuwan awon da ta yi,haka nan kuma bayan ta haihuwa duk zuwa rigakafi za’a bata N500 a kowane rigakafi har ta kamala su.’’

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng