Zaku yi mamakin sunan da sarkin Osun ya sama dan shi
- Oba Oluwa Abdul rahim shine sarki na 16 a masarautar Iwo jahar Osun
- Mai martaba Sarki yana auren wata yar Jamaica wanda ya hau karagar mulki a shekarar 2015
- Ma'auratan sun samu haihuwa satin da ya gabata, kuma sun saka ma dan su Oduduwa
Oba Adewale Abdul rasheed Akanbi shine sarki na 16 a masarautar Iwo jahar Osun. Yana 1 daga cikin abokan Ooni kasar Ife Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi na yarinta.
Ya dare karagar mulkin a shekara ta 2015 kuma yana auren wata mata yar kasar Jamaica mai suna Chin, yar wani tauraro Ludlow Chi.
KU KARANTA:
Sarkin da Sarauniyar sun hadu a kasar Canada inda yake zaune kafin ya dare karagar mulkin. Ma'auratan sun samu haihuwa satin da ya gabata, bayan watanni da sarauniya take dauke da cikin tana yawo a nasarauta, an haifi jaririn a asibiti a kasar Canada.
Yaron da ma'auratan suka samu yazo ana murna sa annashuwa kuma an saka mashi suna Oduduwa . Kamar yadda Yarbawa suka yarda cewa Oduduwa shine asalin samun yankin kasar Yarbawa. Kuma sunan yana nufin abubuwa da dama.
Wannan sunan yayi, muna taya ku murna. Allah ya raya.
Asali: Legit.ng