Ma’auratan da suka fi gajarta a Duniya
An daura auren wasu masoya biyu da suka fi gajarta a duk fadin Duniya a kasar Brazil.
Kimanin shekaru 8 kenan da masoyan wato Amarya Katyucia Hoshino da Ango Paulo Gabriel da Silva Barros dake matukar kaunar junansu suka hadu a shafin yanar gizo.
Sai dai dukkanin ma’auratan wadanni ne, inda aka auna tsawonsu duka akan kafa-5 da inci-8. Masana kundin tarihin Duniya ne suka tabbatar da ma’auratan a matsayin ma’aurata mafi gajarta a duk Duniya.
KU KARANTA: Guardiola yayi da na sanin ajiye Yaya Toure a benci
da fari sun fara haduwa ne ta shafin sadarwa na MSN, inda tun a lokacin ango Paulo yayi kokarin neman Katyucia, sai dai bai samu sa’a ba inda Katyucia ta cire shi daga abokanta. Sai dai bayan shekara daya Katyucia ta sake dawowa da shi cikin jerin abokanta.
Paulo yace, da fari ta dauka ni dan iska ne, amma ina kokarin faranta mata rai ne kawai. A tunaninta ban iya hira ba. Amma bayan ta dawo dani, cikin mintuna 30 muka fara hira, sai tace da alama na kara wayewa.
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng