An gano wadda tafi kowa yawan shekaru a Najeriya

An gano wadda tafi kowa yawan shekaru a Najeriya

Wasu rahotanni na nuna cewa an gano wata mata mai suna Mama Esifiho wadda ake kyautata zaton shekarun ta a duniya za su kai 191 a Najeriya. 

An gano wadda tafi kowa yawan shekaru a Najeriya
Mama Esifiho

Ita dai jikan jikan ta ne mai suna Mr. Avuefeyen shine wanda ya bayyana wa majiyar tamu hakan. Jikan jikan nata dai yace tsohuwa ta kusa shekaru 200 a duniya kuma tana zaune ne a kauyen Ellu dake a jihar Delta.

An gano wadda tafi kowa yawan shekaru a Najeriya

Ku Karanta: Wani dalibi dan shekara 13 yayiwa malamarsa ciki

Da ake tambayar sa sahihancin adadin shekarun na tsohuwar mai ban mamaki, jikan jikan nata ya tabbatar da cewa ta dade sosai a duniya don kuwa har ma ta tsinkayi haihuwar dan jikan jikan ta ma.

Idan har baya nan da aka samu sun tabbata kuwa to babu shakka wannan tsohuwar ita ce mace mafi tsufa da aka taba sani a kasar nan ta Najeriya wadda take da rai.

An gano wadda tafi kowa yawan shekaru a Najeriya

Wannan labarin yana zuwa ne bayan an gano wani mutum a kasar Brazil mai dumbin shekaru har 131 wanda kuma yake zaune da mata 69 tare kuma da ya'ya 3 kacal.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel