'Yan bindiga sun sace matan kwamishina
- An sace mata 2 na wani kwamishina jihar Nassarawa a ‘yan uwansu da abokan arziki na ta addu'oi nane neman dauki daga Allah
- Yayin da su ke sauraron sakon neman kudin fansa bukatun daga wadanda suka sace su ‘yan sanda sun kaddamar da gagarimin bincike na neman 'yan bindigar da kuma matan da aka sace
An sace matan kwamishinan kula da kananan hukumomi da sha'anin masarautu na jihar Nassarawa, Aliyu Tijjani.
Matan su biyu, a cewar wani wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce, an sace matan ne a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba da daddare, yayin da wasu gungun 'yan bindiga kimanin su goma su ka afkawa gidan kwamishinan a garin Nassarawa da misalin karfe takwas na dare.
A lokacin da barayin suka zo gidan, sun rika harbin iska a sama domin firgita jama’a, kafin su kutsa kai cikin gidan su kuma fito da matan, su cusa su cikin mota, su kuma yi awon gaba da su.
KU KARANTA KUMA: Jama’a sun yi tir da halayyyar ‘yan Lagos bisa wannan dalili
Kwamishinan Malam Tijjani ya ce, har yanzu su na nan suna jira su ji daga bakin barayin dangane da bukatunsu, amma har yanzu ba su tuntube su ba.
Ya kuma ce: “Har yanzu da na ke magana da ku, ba mu san ina a ke ajiye da matan nawa ba, kuma ba wanda ya tuntube mu, za mu ci gaba da addu'ar Allah ya bayyana su.“
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Abubakar Sadiq-Bello ya tabbatar da faruwar lamarin,sannan kuma ya ba da tabbacin cewa, “'yan sanda na bin sahunsu, kuma ba da jimawa ba za a kama su da yardarm Allah
“Mun samu labarin faruwar lamarin kuma a yanzu da mu ke magana da ku, mun samo bayanan inda su ke kuma muna gab da cim musu.”
Asali: Legit.ng