Limamin coci yayi watsi da matarsa mai ciki domin fasikanci

Limamin coci yayi watsi da matarsa mai ciki domin fasikanci

Pasto Abrahams wanda ke limanci a cocin Mount Zion Light House Full Gospel Church a garin Utu Nto Obio Ekop yayi lalata.

Da kyar wani pasto yasha daga hannun wasu samari bayan an kama shi yana yin fasikanci da wata mamba ta cocin yayin da matarsa ke cikin nakuda.

A cewar rohotanni daga jaridar INK, 'mutunen Allahn' mai suna Pasto Abrahamas ya jure ma fushin samarin da suka kamashi yana saduwa da matar daya daga cikin mabiya cocinsa.

KUKARANTA: Dalibi mai shekaru 13 yayiwa malama ciki

Pasto Abrahams wanda ke limanci a cocin Mount Zion Light House Full Gospel Church a garin Utu Nto Obio Ekop, a cikin karamar hukumar Etim Ekpo ta jihar Akwa Ibom wanda aka ce yayi watsi da matarsa wadda taje asibiti domin haifuwa yayinda shi kuma ya tafi wajen farkarsa.

Duk da yake Pasto Abrahams sanannen malamin addini ne kuma mai kwazon addu'a kuma kamar uba yake ga matar da maigidanta ya rika yin fasikanci da matar. Asirinsu ya tonu bayan makwabtanta sun ga paston ya dade cikin gidan. Makwabtan sun kama su hannu biyu yayin da suka doki paston suka kuma tafi dashi tsirara tare da matar zuwa dakin taro na garin.

Daga baya an ci shi tarar N200.000, akuya,doya, kayan shaye-shaye da sauran abubuwa bayan mahaifinsa wanda shine babban pasto na cocin yasa baki.

Tofa!! Me ka gani ?

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng