Tafarnuwa Sinadarin soyayya

Tafarnuwa Sinadarin soyayya

Ga mai son lakanin jan hankalin mata su kuma matso kusa da shi, ya gyara zama don jin sakamakon wani bincike da masana suka yi a kan cin Tafarnuwa

Tafarnuwa Sinadarin soyayya
Tafarnuwa da zuma

Masana kimiya sun yi wani gagarimin bincike mai cike da mamaki na wani nau’in abincin da kusan kowa ke gudu, watau Tafarnuwa.

Kamar yadda ya tabbata a wani bincike, cin Tafarnuwa mai yawa na iya sa warin jikin da maza ke yi, jan hankali mata zuwa gare so da kauna, a wani nazari a da wasu masana suka yi, an gwada tafarnuwar a kan wasu mutane farar fata da aka kebe, a inda wasu daga cikinsu a ka ba su Tafarnuwa da yawa, wasu kuma daga cikinsu a ka ba su kadan,  domin su ci na tsawon mako daya.

Daga bisani a ka nemi mata su shinshina jikin mabanbanta mazajen domin tantance warin jikin mazajen da suka fi jan hankalinsu, a inda aka sakamakon ya nuna cewa, hankalin matan ya fi karkata ga wadanda suka ci tafannuwar mai yawa fiye da wadanda suka ci kadan.

KU KARANTA KUMA: Malamar Firamare a Jigawa ta cira tuta saboda wannan dalili

To wannan dama ce gareku, musamman mazaje, idan kana so ka ja hankalin mata? To yawaita cin tafarnuwa. Ka kuma tabbata ka tanadi ‘yar alewa tare da kai in har ba ka son ka ruda matan.

Haka kuma ta tabbata cin Tafarnuwa a yayin juna biyu na taimakawa sosai ga jaririn da ke ciki ya kara nauyi a cikin mahaifa, ta na kuma taimakawa wajen yakar cututtukan da jaririn ka iya dauka ta hanyar iska ta yadda zai karawa kwayoyin garkuwar karfi; hakan zai taimaka wajen yakar cututtukan tari, da sanyi da kuma ciwon kirji.

Cin danyar Tafarnuwa da zuma shi ma zai taimaka wajen rage hawan jinni. Wannan hadin (danyar tafannuwa da zuma) na da kyau wajen duba da kuma daidaita matakin sinadarin da ke cikin jini a jiki.

Don haka, masu cutar hawan jini na iya zunduma cikin wannan tsarin na lafiya.

Lallai ga magani a gonar yaro sai rashin sani.

Ko biyo mu a shafinmu na Tuwita a @naijcomhausa

&t=2s

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng