Yan bindiga sun sace sakataren Jama’atu Nasril Islam
- Bayanai sun nuna cewar an kama malamin ne Sheikh Abdulaziz Yusuf da yammacin jiya kusa da garin Kaduna tare da direban sa yayin da suke hanyar zuwa Kaduna dan shiga tawagar Jama’atul Nasril da za ta je Sokoto domin gabatar da ta’ziyar rasuwar Sarkin Musulmi na 18 Alh Ibrahim Dasuki
- A wani labarin kuma, Wasu 'yanbindiga akan babura sun afkawa kauyuka a karamar hukumar Rafi inda suka kashe mutane shida tare da jikata wasu da dama da kuma yin awan gaba da shanu masu yawa
Bayanai sun nuna cewa maharan sun kai kimanin hamsin kuma bayan sun gama ta'asar a kauyukan Kukoki da Madaka sun yi awan gaba da shanu masu dimbin yawa.
Ku Karanta: Fadar shugaban kasa ta ce a shiryawa matsanaciyar yunwa
Al'amarin ya sa daruruwan mutanen yankin sun tsere daga gidajensu saboda fargaban kada mutanen su dawo su gama dasu. Mutane suna gudun hijira yanzu a garuruwan Pandogari da Kagara.
Malam Ibrahim Gambo daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa wanda yanzu yake garin Pandogari yace yadda suka dinga harba bindigoginsu ya sa kowa ya razana. Da safe ma da suka je su kwashe kayansu samun mota yayi masu wuya.
Shugaban karamar hukumar Rafi Alhaji Gambo Tanko yace tabbas mutanen dake zaune a yankin suna cikin firgita akan hakan ne ma suke barin garuruwansu.
Gwamnatin jihar Neja tace a yanzu haka tana kokarin daukan matakin agazawa wadanda suke kwance a asibiti. Alhaji Ibrahim Ingawa shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar yace karamar hukuma tana kula dasu kuma inda suka kasa zasu tallafa daga nan.
Kwanan nan kananan hukumomin dake arewacin jihar na fama da karuwar fashi da makami dalili ke nan da shugaban karamar hukumar Rijau yayi tayin tukuicin nera dubu dari uku ga duk dan fashin da ya tuba ya kuma mika bindigarsa ga hukumomi.
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng