An ga kifi mai kai biyu

An ga kifi mai kai biyu

An dai bayyana cewar abun mamaki baya karewa, bayan da wasu masana suka gano wani kifi mai kai biyu.

Masanan dai sun ji mamaki kwarai tare da kaduwa kwarai da gaske bayan da suka gano kifin mai kawuna biyu tun lokacin binciken su a 2008.

An ga kifi mai kai biyu
An ga kifi mai kai biyu

Abun da dai shine yanzu ake ta magana dashi a kai, an dai bayyana cewar wasu masana kimiyar kasar Sifaniya ne suka gano wannan halittan mai ban al'ajabin a kogin Atlantic sawtail akaga wannan halittan mai suna Catshark. Sun dai fahimci hakanne ta hanyan binciken da suka gudanar a kwan kifin da suna gano a kogin.

KU KARANTA: Gwamnan Benue yayi kaca-kaca da Sarkin Musulmi

Sai sukayi kokarin bude kwan saboda suyi bincike, inda bayan sun gama binciken da sukeyi sai suka sanya binciken da suka samu nasara samu a cikin kundin bincike na ilimin kimiyyar sanin namun daji da kuma dabbobi.

Alokacin da suka yanke shawarar fitar da kifin daga cikin kwansan sa, sun dai tabbatar da cewar idan basu fidda shi daga ciki ba, to babu shakka mawuyacine kifin ya rayu har a iya kyankyasar sa. Sannan kuma suna da tabbacin cewar mawuyaci ne wannan halittan ruwan yayi tsawon rayuwa a duniya.

Me zakayi idan ka samu irin wannan kifin?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng