Najeriya ce ta Uku a jerin kasashen da aka fi yin ta’addanci
Kwalejin tsimi da tanadi da zaman lafiya ta fitar da jadawalin ta'addanci na Duniya na shekarar 2016, wanda da shi ne ake gane matsayin da ta’addanci ya kai a Duniya gaba daya.
Rahoton ya bayyana Najeriya a matsayin ta Uku, ma’ana zuwa yanzu dai kasar Najeriya bata motsa daga matsayinta na baya ba a bara. Ga jerin kasashen da suka fi matsalar ta’addanci a Duniya.
Duk da cewar Najeriya itace ta Uku a jerin kasashen, amma rahoton ya bayyana cewar an samu raguwar asarar rayuka a Najeriya da kasar Iraqi sakamakon nasarar da Sojoji ke samu kan kungiyar Boko Haram a kokarinsu na murkushe kungiyar, amma yayin da Sojojin Najeriya suke samun nasara kan Boko Haram, sai suka koma kasashen makwabta, kamar su Chadi, Nijar da Kamaru inda suka haihar da asarar rayuka fiye da yadda yake a baya.
“an samu karuwar asarar rayuka a kasar Nijar sosai fiye da misali, inda ashekarar 2014 aka samu rasa rayuka 11 kacal, amma sai gashi a shekarar 2015 an samu asaran rayuka 649 a 2015. Wannan shine samun karuwar asarar rayuka mafi girma da aka taba samu a Duniya, kuma ya faru ne sakamakon fadawar kungiyar Boko Haram kasar ta Nijar” inji rahoton.
KU KARANTA: Soji sama sun yi luguden wuta a Borno
A yanzu dai kasar Nijar itace ta 16 a jerin matsayin kasashen da ta’addanci ya addaba, idan aka kwatanta da matsayin ta na bara na 51, za’a ga cewar an samu karuwar ayyukan yan ta’adda a kasar kenan. Hakazalika ita ma kasar Kamaru ta kara yin sama a jerin inda ta motsa daga ta 14 zuwa ta 20 a shekarar 2016.
Sai dai kungiyar ISIL dake kasar Iraqi ta sha gaban Boko Haram a yanzu a ayyukan ta’addanci, inda take rike da kambun ta’addanci tun a shekarar 2015. Rahoton yace “duk da samun raguwar kashe kashen ta’addanci a Najeriya, amma ana samun yawan kashe kashen irin na rikicin kabilanci ko na addini. Da kuma kashe kashen yayin fafatawa tsakanin Sojoji da Boko Haram, hakan yayi sanadiyyar rasuwar mutane 4,422 a filin daga.”
Rahoton yace, an kiyasat cewar Boko Haram na kashe mutane 11 a duk harin da suka kai, kuma yawanci fararen hula suke kashewa a hare haren. A duk cikin mutane biyar da suka mutu daga harin yan ta’adda, hudu daga ciki fararen hula ne”
“sa’annan duk da cewa an fi amfani da kananan makamai wajen kashe kashen, amma a yanzu ana samun yawaitan amfani da bamabamai, tun bayan samun horo da kungiyar Boko Haram tayi daga Al-Shabab”
“a shekarar 2013 kadai, Boko Haram ta sanya bamabamai a wurare 35, inda ta kashe mutane 107, sai gashi a shekarar 2015 ta sanya bamabamai a wurare 156 tare da kashe mutane 1,683. Kuma kaso 2 cikin 3 na hare haren duk kunar bakin wake ne, wanda kiyasi ya nuna a kowane kunar bakin wake guda, ana kashe mutane 10” inji rahoton.
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng