An kama wasu yan dan fara masu amfani da yanar gizo

An kama wasu yan dan fara masu amfani da yanar gizo

- Yansanda sun kama wasu samari yan shekara 20 su 3 yan danfara masu am fani da yanar gizo

- Kamar yadda muka samu labari hukumar yan sanda ta jahar Oyo sun karayin wani kokari bayan rohoton da mutane suka kawo masu

Wadanda ake zargi Lanre Sadiq dan shekara 26 da Sankammi Daramola dan shekara 28, da Opeyemi Adebayo dan shekara 26 an kama su a maboyar su unguwar Soka da layoyin asiri da karfe 6:30 na safe laraba 16 ga watan Nuwamba.

An kama wasu yan dan fara masu amfani da yanar gizo

Kakakin yan sanda Adekunle Ajisebutu najahar yace dama suna ta kokarin su cafke masu laifin tun ranar talata kafin kama suranar laraba.

KU KARANTA KUMA: 

Ajisebutu wanda yayi magana a madadin kwamishinan yan sanda mista Samuel Adebugyu yace" hukumar yan sanda ta jahar Oyo ta kama mutum 3 yan damfara masu amfani da yanar gizo, wadanda aka fi sani da yahoo boys.

Yace an samu nasarar kama su ne a dalilin mutanen gari da su zo suka ce suna zargin su.

Lokacin da ake tuhumar su, sun amsa laifin su, kuma sunce sun damfari mutane da dama, wadanda suke cewa masu cinikin su ne. Abubuwan da aka samu a hannun su sun hada da na'ura mai amfani da kwakwalwa 4 da layoyi na tsafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng