Budurwa ta siyan ma Saurayinta motar alfarma
Wani mawaki mai tasowa a garin Fatwakwal mai suna Kay Style ya kasa boye farincikin sa bayan budurwarsa ta siya masa makekiyar motar alfarma.

Kay ya bayyana ma budurwar tasa godiyarsa a shafin yanar gizo na Instagram, inda kuma ya jaddada mata soyayyarsa.
Kay yace: “Ba kasa natsuwa, ya kamata in bayyana ma Duniya farin ciki na, haduwata dake shekaru hudu da suka gabata tun muna jami’a alkhairi ne a gare ni. Duk da cewa mutane da dama basu kaunar muyi soyayya, basu kaunar su ganmu tare don kina yarinyar Fasto, amma baki yar da ni ba.

“Kin kasance tare da ni kina bani goyon baya a matsayi na na mawaki mai tasowa tun ranar dana fara, gaskiya masoyiyata nayi matukar mamakin wannan kyautar ta mota, abin yayi yawa.”
KU KARANTA: Masoya sun bata kan kujerar Jirgi

Kay ya karkare godiyarsa da cewa, “nayi na Allah godiyar haduwa dake, nayi alkawarin ba zan baki kunya ba, saboda irin kokarin da kike yi min akan sana’ata ta waka. Allah yayi ma mota ta albarka.”
Mu dai fatan mu Kay ya rike mata amana.
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng