Buhari Shege ka fasa - Tsagerun Neja Delta
- Tsagerun yankin Niger Delta sun ce sun Shege ka fasa tsakaninsu da shugaba Buhari kuma sun sake fasa wani bututun mai a yankin, suna mai cewa wannan somin tabi ne
- Sun kuma gargadi shugaban kasa da ya biya bukatunsu ko koma su shiga yaki gadan-gadan, domin ba za su saurara ba
Daya daga cikin kungiyoyin tsagerun yankin Niger Delta mai arzikin Mai, ta kai hari kan wani bututun Mai na kamfanoni Agip, da Oando, da kuma Shell.
Kungiyar tsagerun ta Niger Delta Avengers ta kai harin ne a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba a wata sanarwa da ta fitar, wacce kuma kakakinta Mudoch Agnibo ya sa hannu, ta kuma ce, barna yanzu ta soma.
Sanarwar wacce Legit.ng ta samu gani, ta hannun Kakakin ta ce, ta kungiya za ta ci gaba da kai hare-hare duk da jibge sojojin da ake yi da kuma ikirarin nasara na rundunar sojin kasar ke yi a kansu.
KU KARANTA KUMA: Muna ci gaba da fasa bututun mai - Tsagerun Neja Delta
Kungiyar ta ce, a cikin sanarwar, “da misalin karfe 11:45 na yamma a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba shekarar 2016, kwararrun ‘yan kai hare-harenmu na rukunin 03 sun kai hari kan bututun Mai mai lamba 1 da 2 da kuma 3 na kamfanonin Agip, da Oando, da Shel,l da ke da karfin samar da Mai kimanin ganga miliyan 300,000 a kowacce rana zuwa tashar fitar da Mai zuwa kasashen waje da ke Bonny a jihar Bayelsa.
“Wannan a matsayin mayar da martani ne ga kai hare-haren soja ne na zalunci da suka sa wa suna yaki ‘cizon kifin shark’ domin ci gaba da zaluntar al’ummar yankin da kuma hanamu walwala, tare da ci gaba da cike aljihunan wasu attajira da kuma jam’iyyar APC da kudade.”
Kungiyar tsagerun a cewar sanarwar, za ta ci gaba da abinda ta kira “wannan Yaki” , kuma ita ba ta kyamar zaman lafiya, sai dai ta na so ne a cimma “zaman lafiya tare da mutunci,” kuma za ta yi hakan ne kawai da zaran an samar da yanayin da ya dace da za su tattauna da shugaban kasa a bisa bukatu 16 da suka gabatar masa a farkon watan nan.
Asali: Legit.ng