Wasu yan Najeriya a Amurka

Wasu yan Najeriya a Amurka

Alkawarin shugaba mai jiran gado na Amurka Donald Trump na korar ‘yan Afrika mazauna Amurka da zaran ya ci zabe ba sabon labrai ba ne, sai dai da akwai wasu yan Najeriya da sabon shugaban bai isa ya koresu ba soboda sun kama kasa

Wasu yan Najeriya a Amurka
Trump ko ina alkawarinsa na korara baki 'yan Africa?

Jude O Nkama: Dan Najeriya kuma dan Afrika na farko da a ranar 6 ga watan Janairu aka nada shi  a mukamin mai Shari’a a tarihin shekaru 349 na birnin New Jersey . Zai yi wahala Trump ya iza keyarsa gida.

Hakeem, Kae-Kazim: Fitaccen mai fitowa a fina-finai ne, a kadan daga cikinsu shi ne wasan talbijin na Starz na Black Sails  da kuma fitowarsa a matsayin George Ratanga a fim din Hotel Rwanda na Shekarar 2004. Baya ga wannan dan asalin Najeriyar shine jakadan kungiyar mai zaman kanta ta Africa 2.0 wacce ke da rajin ganin an samar da ingantaccen jagorancin a nahiyar Africa.

Wale: cikakken sunansa shi ne Olubowale Victor Akintimehin da aka Haifa a shekara 1984, asalinsa dan Najeriya ne, kuma ya yi suna a wake-waken zamani salon Rapp. Tauraruwarsa ta haska ne a shekara 2006, bayan wata waka da ya yi mai suna Dig dug” (Shake it).

Wale yayi fice matuka a inda ya fito a shiryen gidajen talbijin daban-daban na kasa ciki har da MTV da sauran wasu manya-manyan jaridu na bakaken fata.

Uzo Aduba: Cikakken sunanta shi ne Uzoamaka Nwanneka “Uzo” wacce aka haifa a 1981, ‘yar wasan kwaikwayo ce, kuma mawakiya. Ta samu kyautuka na yabo daga irin wasannin da ta fito, iyayenta ‘yan asalin Achi ne daga jihar Enugu.

Samuel Ifeanyi : Dan asalin jihar Legas ne, mahaifinsa dan Najeriya, mahaifiyarsa kuma baamurkiya,  Dan siyasa ne, kuma dan jam’iyyar Democrat daga Indianapolis, Indiana. Yana daya daga cikin majalisar birnin Indianapolis daga gunduma ta 15 ta kudu maso yammaci, kuma tsakiyar birnin. A ranar 22 ga watan Disamba na shekarar 2011, mai shari’a na jihar ya ayyana shi a mukamin  magatakardar jihar.

Kadan ne daga cikin ‘yan Najeriya masu rike da muhimman matsayi da kuma mukamai wanda kasar Amurka ke amfana da su matuka, wanda zai yi wuya sabon shugaban ya iza keyarsu zuwa gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng