Wani yaje cire kudi ATM abunda ya faru a gaba
Abunda za'a iya dauka a matsayin al'ajabi na bikin Kirismeti , mashin din ATM ya ya cigaba da feso kudi, sai kawai abun ya zama abun mamaki a rayuwar shi, ta yadda mashin din ATM din ya cigaba da sako mai kudi.
Wani wanda ke amfani da ATM ya samu goron Kirismeti.
Kamara ta cctv ta nuna wani mutum da gilashi da hula ki Sallah yana tafiya a zuwa mashin din ATM dan ya cire kudi a kasar Malaysia.
Sai dai bayan ya gama cire kudin, sai ya samu wani abu na ban mamaki a rayuwar shi a yayin da mashin din na ATM ya cigaba da yin aman kudi.
A abunda ya zama kamar ranar da yafi komai sa'a a rayuwar shi inda mashin din yayi aman kimanin kudin Malaysia har dala dubu 10000.
Mutumin da ba'a bayyana ko waye ba be yi wata wata ba ya cigaba da tattara kudin da suke fita daga ATM da sauri saurin shi.
Har lokacin da ake tattara labarin nan, ba'a san ko mutumin ya dawo da kudin ba ko ya tafi da su ko kudin daga asusun ajiyar shi ya fito.
Asali: Legit.ng