Ta fado daga bene hawa 9, bayan sharholiya da Saurayinta

Ta fado daga bene hawa 9, bayan sharholiya da Saurayinta

Wata budurwa yar kasar Birtaniya ta fado daga wani dogon benen gidan hutawa bayan sun hole da saurayinta.

Ta fado daga bene hawa 9, bayan sharholiya da Saurayinta
Hall da benen da ta fado

Budurwar mai suna Danielle Hall ta fado ne daga hawa na 9 na wani gidan shakatawa mai suna Bermuda dake garin Benidorm na kasar Sifen bayan sun sha sharholiya da saurayinta.

Ita dai Hall ta fita da saurayinta ne zuwa wurin shakatawa dake gabar tekun Costa Blanca tare da saurayinta dan shekaru 23 mai suna Jordan, gabanin mutuwarta. Rahotanni sun bayyana cewar masoyan sun sha barasa sunyi tatil bayan sun sha sharholiya, cikin mayen barasa ne Hall ta fara tangali tangal, sai kawai ta fado daga hawa na 9 na benen, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safe, koda aka kira yansanda ta rigaya tace ga garinku nan.

KU KARANTA: Wani mutum ya kashe agolarsa

Rahotanni sun bayyana cewar kakar Hall ita ma ta kama daki a gidan hutawar, sakamakon sun yi niyyar kwashe mako guda suna shakatawa ne a gabar tekun.

Wata majiya ta bayyana mana cewar, ma’aikatan gidan hutawar sunyi matukar kaduwa da farywar lamarin. Ita kanta ma’aikaciyar data baiwa Hall dakin da take zaune a ciki ta tsargu, inda aka jiyo ta tana kuka tana fadin idan da ta basu daki a hawa na 1 ko na 2 da Hall bata mutu ba.

Dayake majiyar tamu ta ga lokacin da Hall ke fadowa daga benen, tace ta gagara barci tun lokacin da lamarin ya faru. Yansanda sun yi ma shaidun gani da ido tambayoyi, tare da saurayin Hall da kakarta. Sa’annan yansandan sun ce mutuwar yafi kama da hadari ba daukan rai ba.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng