Wani Saurayi ya baiwa budurwsa kyautar Marsandi
Wani Saurayi dan Najeriya mai matukar kaunar budurwarsa yayi mata maganin matsalar shiga motar haya.
Wannan gwanin soyayyan ya siya ma budurwsa tsaleliyar mota kirar marsandi sabuwa a leda ne sakamakon baya jin dadin yadda take wahalar neman abin hawa idan zata tafi zuwa aiki a kulli yaumin. Saurayin yayi mata kyautan ne a ranar cikarsu shekaru 2 da fara soyayya.
Budurwa ta kasa hadiye farin cikin ta inda tayi rubutu kamar haka a shafin ta na Facebook “abinda ke biyo baya kenan idan kika samu saurayi tsoron Allah, mai matukar kaunar ki, wanda yake muradin aurenki. Wannan shine mijina, abin kaunata”
KU KARANTA: Kalli ‘Muhammed Buhari’ a cikin tsarin MMM?
Ta cigaba da fadin, “nagode ma Allah! Dama yan watannin nan a tasi ko jirgin kasa nake zuwa aiki, amma ban taba yi mai korafi ba. Sai gashi yau an kawo min wannan! Nayi murnan cikar soyayyar mu shekaru 2. Kuma yan mata ku cigaba da nema, wata kila kudace.”
Asali: Legit.ng