MOSOP tayi Allah wadai da matakin soja kan 'yan Ogoni 9

MOSOP tayi Allah wadai da matakin soja kan 'yan Ogoni 9

MOSOP a yau tana juyayin wadanda suka sadaukar da rayuwarsu kan gwagwarmayar Ogoni

MOSOP tayi Allah wadai da matakin soja kan 'yan Ogoni 9

Kungiyar 'yan rajin Ogoni koko Movement for the Survival of the Ogoni People (MOSOP), kungiyar dake jagorar ci gaban mutanen Ogoni dake jihar Rivers ranar Alhamis tayi nazarin rayuwar Ken Saro Wiwa kuma tayi kira ga 'yan Najeriya da subi hanyar lalama irin wadda Saro- Wiwa ya fifita.

A wata sanarwa da Legit.ng ta samo daga sakataren watsa labarai na MOSOP.

KU KARANTA: Buhari ya bada umurnin sallaman ma’aikatan gwamnati

Fegalo Nsuke, gungun ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta duba hukuncin kisa wanda aka yima wasu 'yan Ogoni 9 daga gwamnatin mulkin soja a shekarar 1995.

Sanarwar na cewa "MOSOP a yau tana juyayin wadanda suka sadaukar da rayuwarsu kan gwagwarmayar Ogoni, wadanda sukayi fice sune Ken Saro Wiwa, Saturday Dobee, Nordu Eawo, Daniel Gbooko, Paul Levera, Felix Nuate, Baribor Bera, Barinem Kiobel, da John Kpuine.

"Yau muna juyayin sadaukar wa na gwarajen mu, yana nuna rashin laifinsu da kuma irin shari'ar da akayi masu maras adalci da kuma saurin kashe su da gwamnatin Najeriya tayi masu ranar 10 ga Nuwamba 1995."

Ku biyo mu ta shafin sada zumuntar mu na Twitter a @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng