'Yan shi'a sun kara da 'yan sanda

'Yan shi'a sun kara da 'yan sanda

- A wani labari da dumi-duminsa, wasu fusatattun ‘yan  kungiyar ‘Yan Shi’a  sun yi arrangama da ‘yan sanda a Kano a cewar Premium Times

- An rade-radin an hallaka wani dansanda yayin wasu 'yan shi'a suka rasa rayukansu, an kuma datse babbar hanyar zuwa Zaria mai muhimmanci saboda hargistin 

'Yan shi'a sun kara da 'yan sanda
Wasu membobin kungiyar Shia

Wasu mabiya mazhabin Shi’a a Kano sun yi arangama da ’yan sanda a ranar Litinin 4 ga watan Nuwamba shekarar 2016, ana kuma rade-radin cewa wasu su da dama daga cikinsu sun rasa rayukansu.

A Rahoton da kafar yada labarai ta PremiumTimes ta yada a shafinta na intanet ta ce, rahotanin da ta ke samu na nuna cewa, an yi arrangamar ne a tsakanin ‘Yan Shia’a da kuma ‘Yan sanda a wajen Kano daidai garin Tamburawa, kan Titin zuwa Zaria da yau din nan.

Rahoton ya kuma ce, an hallaka wani dan sanda, su ma ‘yan shi’an sun rasa rayukan ‘yan uwansu da ba san ko nawa ne ba, a yayin arangamar.

KU KARANTA KUMA: Shi’a: Jihohin arewa 5 da ka iya haramta tarukan addini

 

'Yan shi'a sun kara da 'yan sanda
'Yan shi'a sun kara da 'yan sanda
'Yan shi'a sun kara da 'yan sanda

 

Rahoton ya ci gaba da cewa, wani mazunin yankin wanda ya shaida lamarin ya ce, ‘Yan sanda sun yi arangama ne da ‘yan Shi’an, a kokarinsu na hana wani tattaki da ‘yan Shi’an suke yi.

An kuma karo yawan jami’an tsaro yayin da hargitsin ya sa aka datse babbar hanyar ta gwamnatin tarayya da hade Kano da sauran manyan jihohin kasar ciki har da Kaduna, da Abuja, da kuma Lagos.

A ‘yan kwanakin nan dai, ‘yan kungiyar ta Shi’a sun matsa kaimi da zanga-zanga don neman a sako shugabansu Ibrahim Zakzaky wanda gwamnati ke tsare da shi.

‘Yan kungiyar sun kuma gudanar zanga-zanga a manyan biranen kasar ciki har da babban birin tarayya Abuja, inda yan sanda suka tarwatsa su da barko non tsohuwa mai sa hawaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel