Aguero ya bayyana fushin Messi bayan wasa

Aguero ya bayyana fushin Messi bayan wasa

Manchester city ta lallasa Barcelona da ci 3-1. da kuma an yi rohoton cewa Messi ya zagi wani dan wasar Man city, kamar yadda Aguero ya bayyana lamarin. 

Dan wasan Manchester city Sergio Aguero ya bayyana cewa Messi yayi fushi bayan an lallasa kungiyar shi ta Barcelona.

Kungiyar Manchester city ta lallasa Barcelona da ci 3-1, a wasar dai Messi ya fara zura kwallo a ragar city, daga bisani Gandogun ya jefa wasar farko a wasar da Aguero ya taimaka mai ya zura, sai kuma De Bruyne ya kara na 2 inda ya jefa na 2, sai wanda yafi kowa a wasar wato Gundogun ya kara da na 3.

Aguero ya bayyana fushin Messi bayan wasa
Lionel Messi

Wani rohoton da muka samu wanda ba mu tabbatar ba cewa Messi yayi fada da yan wasar Man city bayan wani wanda ba'a fadi sunan shi ba yace mai wani abu yayi da suke fita filin, kamar yadda rohoton ya zo mana ance Messi ya maida martani har ya kira shi da mara tunani.

Kamar yadda rohoton Mirror suka bayyana ance Messi yabi wannan dan wasan inda yake cemai ya dawo nan kada ka boye, kafin abokin wasar shi na kasar su Aguero yazo ya bashi hakuri, da kuma yimai duka sau 2 na wasa a kirjin shi dan kwantar mai da hankali.

Aguero ya bayyana cewa Messi bayan sakamakon wasar be ji dadi ba, amma ban san me ya faru ba, da na tambaye shi sai yace man wani abu ne da be dace ba akayi mai. Ko da naje gurin yana cikin fushi.

Ya kara da cewa wanda abunda kawai nayi shine kokarin kwantar mai da hankali, kawai dai nayi kokarin canja firar zuwa labari kan tafiyar mu Sao Paolo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel