Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)

Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman labaran da suka girgiza duniya a jiya, Laraba 6 ga watan Nuwamba 2016.

1. Donald Trump ya lallasa Hillary Clinton, ya lashe zaben

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)
Donald Trump

Sabuwar labarin da ke shigowa yanzu na nuna cewa dan takaran shugaban kasan Amurka karkashin jam’iyyar Republican, Donald Trump ne zakaran zaben yayinda ya lallasa Hillary Clinton yar takaran jam’iyyar karkashin jam’iyyar Democrats.

2. Tsarin jam'iyyu masu yawa shi ya dace da Najeriya - Buhari

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)
Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ranar Talata 8 ga Nuwamba yace tsarin jam'iyyu masu yawa shine abinda ya dace da damokradiyyar Najeriya in akayi la'akari da banbance-banbancen al'ummominta.

3. Shugaban kasan Rasha,Vladimir Putin ya taya Trump murna

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)
Trump and putin

Shugaban kasa Rasha, Vladimir Putin ya taya hamshakin attajiri Donald Trump murnan lashe zaben shugabancin kasar Amurka.

4. Dan sanda ya kashe abokin aikinsa akan N20, 000 a Bayelsa

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)

An bada rahoton cewa wani dan sanda a jihar Bayelsa ya harbi daya daga cikin abokan aikinsa dan sanda har lahira a kan kudi N20,000 bayan sunyi sa’insa akan yadda za’a raba kudin.

5. Dangote zai dau Karin sabbin ma’aikata 250,000

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)
Alhaji Aliko Dangote

Kamfanin Wannan hamshakin attajirin, Alhaji Aliko ~Dangote ta sanar da cewa zata samar da aikin yi 250,000 ga yan Najeriya bayan kamala ayyukan.

6. Majalisan dattawa na binciken Amaechi akan kwangilan titin jirgin $2 billion

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)
Rotimi-Amaechi

Majalisar dattawa ta ce Rotimi Amaechi ya saba doka wajen cinikin ginin titin jirgi. Majalisar dattawan ta yanke shawaran cewa zata binciki ministan Sufuri ,Amaechi akan laifin bin hanyar da ya kamata wajen cinikin hantar Fatakwal- Maiduguri da Legas-Kano ga kamfanin Amurka.

7. Tsohuwa ‘yar shekara 132 ta tona asirin Oshiomhole

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)
Madam Veronica Uloko

Wata tsohuwa tukuf yar shekara 132 mai suna , Madam Veronica Uloko,ta bayyana wasu asiran

8. Farfesa ya tube zindir cikin aji

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)

Dalibai a Makhachkala, a kasan Rasha, sun ga wani abun mamaki bayan wani farfesan ilimin jikin mutum ya tube zindir cikin aji yayinda yake koyar da dalibai.

9. Biafra: Kotu ta sa ranar yanke hukunci kan belin Nnamdi Kanu (hotuna)

Labaran da suka girgiza duniya a jiya (Ku karanta)

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta aje Alhamis 17 ga Nuwamba zama ranar yanke hukunci kan bukatar bada beli daga shugaban 'yan rajin Biafra koko Indigenous People of Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng