Budurwa ta hallaka kanta kan saurayi

Budurwa ta hallaka kanta kan saurayi

Wata budurwa yar kasar Zimbabwe ta hallaka kanta bayan saurayinta dan Najeriya ya yaudareta, ya rabu da ita, bayan ya dibga mata ciki.

Budurwa ta hallaka kanta kan saurayi
Elizabeth Choto

Budurwar mai shekaru 27 mai suna Elizabeth Choto dalibace a jami’ar Cyprus, an tsinci gawarta ta reto daga saman silin a dakinta dake rukunin dakunan kwanan yan mata na jami’ar, an ruwaito Choto ta kashe kanta ne bayan ta bayyana ma saurayinta zancen tana dauke da cikinsa, shi kuma sai ya rabu da ita, sakamakon hakan ta kashe kanta.

Hukumar jami’ar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta wani sanarwa data fitar tana cewa “wata dalibar jami’ar Cyprus yar kasar Zimbabwe mai suna Elizabeth Choto ta hallaka kanta. Mun tabbatar da kasancewar dalibar tana zaune a dakunan kwanan na yan matan jami’ar A2 Block. Muna bukatan dalibai dasu kwantar da hankulansu yayin da bincike ke gudana don gano musabbabin mutuwarta.

KU KARANTA:Yadda mu ke yin fashi da makami

“a yanzu haka ana binciken gawar tata, kuma zuwa ranar sabar 5 ga watan Oktoba zamu fitar da sanarwar a hukumance dangane da abin da aka gano. Zamu cigaba da tuntuban ku.”

Budurwa ta hallaka kanta kan saurayi
Elizabeth Choto

Wani dalibin makarantar daya bukace a sakaya sunansa ya tabbatar da maganan tana da ciki, inda yace amma saurayinta ya musanta cikin sa ne. “na san Choto, saboda muna cikin kungiya daya na yan kasar Zimbabwe, mu muka fara samun labarin mutuwarta” inji dalibin.

Dalibin ya cigaba da fadin “abinda ya faru shine ta samu matsala da saurayinta bayan ta bayyana masa tana da ciki. Nan da nan saurayin ya rabu da ita, kuma ya musanta ikirarin ta na cewa shine yayi mata ciki. Sai kawai ta kashe kanta.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng