An haifi jariri ba tare da dubura ko mazakuta ba
An bayyana hotunan wani jariri da aka haifa a garin Onitsha wanda yazo ba tare da dubura ko mazakuta ba, hakan ya sanya likitoci rasa gane jinsin jaririn.
Domin samun damar yin fitsari da kashi, sai da likotoci suka yi tiyata a cikinsa, ta haka ne aka fitar da fitsarin da kashin.
Wannan hali da wannan sabon haihuwar ya sanya iyayen sa Charles Ibeh siyar da dukkanin abinda suka mallaka tare da dakatar da yayansu uku zuwa makaranta sakamakon kudaden da suke kashewa wajen duba lafiyar jaririn, ko jaririya za’a ce.
KU KARANTA: Barnar da harin tsagerun Neja Delta ke haifarwa
Wannan lamari mai cike da al’ajabi ya samo asali ne tun lokacin da Uwar mai suna Uchenna Ibeh ta fara nakuda, inda aka garzaya da ita wani asiti mai zaman kansa a garin Onitsha, a nan aka gano cewar dan nata yazo da nakasa, saboda gabadaya hanjinsa a waje yake, kuma an kasa gano duburarsa da mazakutarsa.
Iyayen wannan jariri na rokar jama’a, kungiyoyi da gwamnatoci dasu taimaka musu, sun bada adireshin su kamar haka “Charles and Uchenna Ibeh, No 19b Old Hospital Road, Onitsha, Anambra State, Nigeria. Lambar waya: 08037773562”
Sai dai, likitoci a asibitin koyarwa na tunawa da Nnamdi Azikwe dake jihar Anambra sun shiga rudani kan yadda zasu shawo kan lamarin wannan jariri.
Asali: Legit.ng