Maciji a cikin jirgin sama a Mexico

Maciji a cikin jirgin sama a Mexico

Wani maciji mai dafi ya a kunno kai a cikin wani jirgin sama a yayin da ya ke tsaka da tafiya a sararin samaniya a kasar Mexico

- Hankalin Fasinjoji ya tashi a yayin da suka ga macijin ya bullo ta saman kujerunsu yana reto a kokarinsa na saukowa cikin jirgin a sama

Hankalin fasinjoji a wani jirgin saman Kamfanin Aeromexico da ya taso daga Torreon zuwa birnin Mexico ya dugunzuma a lokacin da wani katon koren maciji ya bayyana a cikin jirgin da ya ke tsaka da tafiya a sararin samaniya.

Maciji a cikin jirgin sama a Mexico
Koren maciji a cikin jirgin sama da ya ta da hankalin fasinjoji a kasar Mexico

Macijin da aka ce mai dafi ne, ya fito ne daga cikin ‘yan akwatunan da ake ajiya kaya na cikin jirgin da ke saman kujerun da fasjinjojij suke zaune, ya tayar da hankalin fasinjojin da kuma ma’aikatan da ke cikin jirgin.

Al’amarin wanda ya faru a ranar Lahadi 6 ga watan Nuwamba, daya daga cikin fasijojin jirgin ne ya dauki hoton bidiyon tashin hankalin da suka gani a cikin jirgin a lokacin da ya ke tsaka da tafiya a sama, ya kuma saka shi a shafukan intanet, a inda ya ja hankalin duniya.

Maciji a cikin jirgin sama a Mexico
Macijin na kokarin saukowa cikin jirgin daga inda ya ke boye

Hoton bidiyon ya nuna macijin mai matukar dafi da ake kire ‘Viper’ da turanci, ya kai tsawon mita 1.5, yana kuma reto a saman kujerun fasinjojin daga cikin ‘yan akwatunan ajiyar kaya, ga kuma fasinjoji na ta ihu da sowa a cikin tsoro da firgici.

Wanda ya dauki hoton lamarin mai suna Indalecio Medina ya ce, an samu nasarar kama macijin da taimakonsa, “Allah Ya taimake ni na kame macijin da dabara  ta hanyar amfani da wani bargo…”

Jirgin ya samu sauka lafiya a tashar jiragen sama na birnin Mexico jami’ai masu kula da dabbobi suka yi aikinsu na dakume macijin.

Mahukuntan kula da sufurin jiragen sama ta kasar da kuma kamfanin jirgin Aeromexico na daukar matakan da suka dace na ganin hakan ba ta sake faruwa ba, ta hanyar binciken yadda aka yi macijin ya shiga jirgin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng