Kalli matar da ke sadakan abinci a cikin wannan matsin tattalin arzikin
1 - tsawon mintuna
A lahira, babu matsin tattalin arziki.
Hotunan wata mata ya yadu a yanar gizo wanda yake nuna yadda take taimaka wa talakawa da abinci mai dadi.
Hoton da aka daura a shafin Instagram , ya nuna ta tana basu abinci cikin kwano kuma suna layi domin su karba sanwa.
KU KARANTA: Abubuwa 6 na mamaki game da Kanar Abu Ali
Da aka tambaye ta akan dalilin da yasa take haka cikin wannan mugun halin matsin tattalin arzikin da ake ciki, tace a lahira, babu matsin tattalin arziki.
Hitin dai ya yadu a yanar gizo kuma mutane da dam na yabon ta kuma suna mata addu’a da wannan halin kirkin.
Asali: Legit.ng