Dan bindiga ya kashe masu kallon kwallo 13
Wani dan bindiga a kasar Sudan ta kudu ya kashe kimanin mutane 13 dake kallon kwallon gasar firmiya da aka fafata tsakanin Chelsea da Everton a karshen makon daya gabata.
Jaridar Yahoo Sport ta ruwaito mataimakin Kaakakin hukumar yansanda Kwacijwok Dominic Amondoc yace yawan mutanen da suka rasa rayukansu yayin harbin sun haura zuwa 13 sakamakon wasu da suka jikkata a harin suma sun mutu.
Amondoc yace akwai sauran mutane 10 dake samun kulawa a asibiti. Wani daga cikin wadanda suka ji raunuka daga harbin Wani Patrick yace “lokacin da ya harbe ni, sai na fadi kasa warwas, amma sai wasu matasa ma suka fado kai na, haka na kasa dagowa har sai da ya karar da harsashinsa, jama’a da dama sun mutu”
KU KARANTA: An lakada ma wani Soja duka a Warri
Ana tsammanin dan bindigan a buge yake, wato sai da ya sha giya yayi tatil. Da fari ya nuna bacin ransa kan an hana shi shiga gidan kallon kwallon, saboda yace sai dai ya shiga kyauta ba zai biya kudi ba, alhali kudin shiga gidan kallon $0.50, kwatankwacin N230.
Da yaga ba za’a kyale shi ya shiga bane, sai ya koma gida ya dauko bindiga ya dinga harbin mai kan uwa da wabi” inji Amondoc.
Sai dai zuwa yanzu ba’a san inda dan bindigan ya shige ba, amma an fara gudanar da bincike, inji Mataimakin Kaakakin gwamati Paul Akol Kordit.
A wasan da lamarin ya faru Chelsea tayi lagalaga da Everton da ci 5-0 a filin wasa na Stamford Bridge mallakan Chelsea, inda Eden Hazard yaci kwallaye 2, sai Diego Costa, Marcos Alonso da Pedro Rodriguez suka zura daya daya.
Asali: Legit.ng