An yi Jana'izar Abu Ali
An yi jana’izzar jan gwarzo kuma sarkin Yaki da Boko Haram Laftanar-Kanar Muhammad Abu Ali a Abuja, Babban hafsan sojojin Najeriya Laftanar-Janar Tukur Buratai ne ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari a taron karbar gawar a filin jirgin saman Abuja.
An yiwa marigarayin hidimar binnewa ta kasaita, ta kasa da shi da sauran wadanda aka kashe su tare a lokacin da suke aratabu da ta’adda.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Lt.Kanal Abu Ali
Marigayi Kanar Abu Ali ya rasu ne bayan da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi mi shi da wasu sojoji da yake jagora kwanton Bauna a makon da ya wuce.
Gwarzon sojan ya gamu da ajalinsa ne a Mallam Fatori, daya daga cikin manya-manyan garuruwan ‘yan ta’adan da ke bangarn arewa mai nisa a jihar Borno, suka yi katutu.
Rahotanni na cewa, Kanar din wanda ake yi masa lakabi da ‘Sarkin Yaki’, an yi masa ruwan harsasai ne a lokacin da ya ke kokarin fatattakar ‘yan ta’adar daga kokarinsu na kai hari a garin Malam Fatori.
A shekarar 2015 marigayin wanda shi ne kwamandan mayakan bataliyar 272 na tankokin yaki, ya samu karin girma ninkin-ba-ninki daga Babban Hafsan sojojin Najeriya Tukur Buratai saboda jarumta da kuma kwazo a filin daga.
Babban kwamandan askawaran Najeriya kuma shugaban kasa Muhammdu Buhari, ya aika da sakon ta’aziyya ta kashin kansa ga iyalan Kanar din, tare da umartar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari, da ya wakilce shi a taron jana’izzar.
Domin nuna alhininsu dangane da wannan babban rashi ‘Yan Najeriya sun fito da mauru’in #RIPMuhammadAbuAli na ta’aziyya a dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter.
Mu ma a Legit.ng na mika ta’aziyyarmu ga al’ummar Najeriya bisa wannan babban rashi na gwarzo, jarumi kuma ‘Sarkin yaki’ da ‘yan ta’addan Boko Haram, Allah Yayi masa rahama.
Asali: Legit.ng