An  wasta ma wata budurwa sinadarin acid

An  wasta ma wata budurwa sinadarin acid

Bayan ta amince ta auri wani wanda yake da mata, wata budurwa na can rai hannun Allah.

An  wasta ma wata budurwa sinadarin acid

Yarinyar 'yar shekara 25, Ogochukwu Nwosu, tana fama da ciwo mai radadi da bata taba ji ba bayan wani wanda ba'a sani ba ya watsa mata sinadarin acid.

KU KARANTA: An nemi wani Gwamna an rasa

Ogochukwu wadda ke kwance a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Lagos a Idi-Araba na kan hanyar dawowa gida daga aiki ta tsaya a tashar mota dake Ilasa kan titin Oshodi-Apapa yayin da wani mutum yazo bisa babur, ya watsa mata sinadarin, ya kuma tsere kan babur dinsa. Masu wucewa suka garzaya da Ogochukwu zuwa asibiti inda aka tabbatar da cewa ta sami kuna a fuskarta, wuya da nono da kuma wasu sassa na jikinta.

Yayin da take magana da Punch Metro, Ogochukwu tace tana zargin matar mutunen data amince ta aura mai suna uwargida Chidi Ogocukwu ta kara da cewa ta yi mata barazana sau da yawa ta hanyar waya da sakon kar ta kwana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel