Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman labarai da suka faru a Najeriya a karshen makon da ya gabata

1. Uwa,’ya, da jika sun hallaka a hadarin kwale-kwale

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Akalla mutane 7 ne suka rasa rayukan su a wata hadarin jirgin kwale-kwale da faru a rafin Gbako a Karamar hukumar Katcha a jihar Neja.

2.‘Yan Najeriya na bakin cikin kisan Kanan Abu Ali da Boko Haram tayi

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Labarin da aka samu a safiyar jiya, 5 ga watan Nuwamba akan kisan Laftanan Kanal Muhammad Abu ali , ya tayar da bakin cikin a fadin kasa ga baki daya.

3. Matsin tattalin arziki ya hana shigowa da motoci Najeriya

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Matsin tattalin arziki da wahalan canjin kudi ya shafi sana’ar  shigo da motocin Najeriya ta tashar jirgin ruwa. Game da cewar Manajan ayyuka na ma’aikatar tashan jirgin ruwa, Mr Jack Angrish ne ya ce shigo da kaya ya ragu daga 30,000 zuwa 6,000 a watanni 6 da suka gabata.

4. Dukkan ku zabi ne – MASSOB ga shugabannin Igbo

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako
(MASSOB)

Kungiyar fafutukar neman Biafra wato Movement for the Actualization of Sovereign State of Biafra (MASSOB) ta siffanta wadanda basu goyon bayan manufar Igbo na samun yanci a matsayin zabi.

5. Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane 5 a jihar Ekiti

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Anyi garkuwa da mutane 5 a jihar Ekiti, jihar mai maganan nan Ayo Fayose a ranan asabar, 5 ga watan Nuwamba 2016. Game da cewar NAN, wadanda akayi garkuwa da su sune Fasto Ojo da direbansa da kuma wasu guda 3.

6.Sanata Omisore yayi aman N350m ga EFCC

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun ya dawoda kudi N350m daga cikin N1.7 billion na rashawan zaben jihar Ekiti da kuma badakalar kudin makamai zuwa ga hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta yi masa

7.EFCC ta haramta kawowa Fani-Kayode ziyara

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta haramta kawo ma firsinoni ziyara. Jaridar vanguard ta bada rahoton cewa an hana dukkan firsinonin EFCC kiran iyalan su da amsoyan su.

8.Babban titin Lagos- Ibadan ya samu lafiyar tafiya - FRSC

Abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen mako

FRSC tana tabbatar ma masu bin titin Lagos - Ibadan cewa motoci zasu iya zurga-zurga duk da gyaran da ake a sashen da yafi cinkoso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng