‘Yan Najeriya na bakin cikin kisan Kanal Abu Ali da Boko Haram tayi

 ‘Yan Najeriya na bakin cikin kisan Kanal Abu Ali da Boko Haram tayi

Munyi matukar bakin cikin rashin daya daga cikinmu wanda ya zage dantse

- An kashe Ali da wasu soji guda 4 ne a ranan Juma’a, 4 ga watan Nuwamba

 ‘Yan Najeriya na bakin cikin kisan Kanal Abu Ali da Boko Haram tayi

Labarin da aka samu a safiyar jiya, 5 ga watan Nuwamba akan kisan Laftanan Kanal Muhammad Abu ali , ya tayar da bakin cikin a fadin kasa ga baki daya.

An kashe Ali da wasu soji guda 4 ne a ranan juma’a,4 ga watan Nuwamba yayinda sukayi wata artabu da yan tda kayar bayan Boko Haram. Kanal KUkasheka ya bayyna haka a wata jawabi.

KU KARANTA:Rabi’u Kwankwaso ya gana da Shugaba Buhari

Ali, wanda ya ci lambar yabon shugaban rundunar soji akan karfin hali da kokari ,wanda ya jagorancin farmakin kwato Gamboru-Ngala, Baga da kuma wasu garuruwa.

Rasuwan shi ya zo ne lokacin da rundunar soji na karasa sharan yan Boko Haram daga inda suke buya a cikin jihar Borno.

Kwamandan tiyatan Operation Lafiya dole, yace: “Ali ya bauta ma kasar da sosai,ya rasa rayuwarsa saboda miliyoyi su kwanta cikin lafiya.

"Munyi matukar bakin cikin rashin daya daga cikinmu wanda ya zage dantse wajen ganin cewa an fitar da yan ta’adda daga arewacin kasar.

Wasu yan Najeriya su garzaya kafofin ra’ayi da sda zumunta domin nuna juyayinsu game da wannan rashi da akayi.

 “Allah jikan Lt Colonel Muhammad Abu Ali da kuma dukkan sojin da suka rasa rayukansu domin karemu. Yunkurin ku ba zai tafi a banza ba.

“Abun bakin cikin,munyi rashin wani babban hafsan soja, Lt Colonel Muhammad Abu Ali da wasu 4 sun mutu yayin artabu da yan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng