Matsin tattalin arziki ya hana shigowa da motoci Najeriya

Matsin tattalin arziki ya hana shigowa da motoci Najeriya

- Matsin tattalin arziki da wahalan canjin kudi ya shafi sana’ar masu shigo da kaya Najeriya

- Yawan motocin da ake shigowa dasu ta jirgin ruwa ya ragu yanzu

- Manajan ayyuka na ma’aikatar tashan jirgin ruwa, Mr Jack Angrish ne ya bayyana hakan

Matsin tattalin arziki ya hana shigowa da motoci Najeriya

Matsin tattalin arziki da wahalan canjin kudi ya shafi sana’ar  shigo da motocin Najeriya ta tashar jirgin ruwa.

Game da cewar Manajan ayyuka na ma’aikatar tashan jirgin ruwa, Mr Jack Angrish ne ya ce shigo da kaya ya ragu daga 30,000 zuwa 6,000 a watanni 6 da suka gabata.

KU KARANTA: PDP tace dole Shugaba Buhari ya kori wadannan Ministoci

Angrish yace tsadar dalar Amurka akan kudin Najeriya ne ya shafi sana’ar a wannan lokaci. Yayi jawabi ne a jiya,5 ga watan Nuwamba a jihar Legas.

Yace: “Wannan lokaci ne da ya kamata masu kasuwancin mota su ta tara kudadensu domin tabbatar da ana hada mota a Najeriya.

“Shigo da motoci ya ragu daga 30,000 zuwa 6,000 a watanni shida da suka gabata wanda yayi sakamamon rasa ayyukan wasu ma’aikatan tashan jirgin kasan.

A bangare guda, Dirakta manajan kamfanin man fetur na Capital Oil kuma mai kamfanin jaridan Authority, Dr Ifeanyi Ubah,ya siffanta kansa a matsayin babban masanin tattalin arziki a Najeriya.

Dr Ifeanyi Ubah ya baiwa shugaba Buhari shawara akan yadda za shawo kan matsalan dala da Naira a kasar.

Dr Ifeanyi Ubah wanda yayi jawabi a wata taron matasa a jiharsa yace babu abinda ya faru da tattalin arziki Njaeriya amma matsalan shine babu masana tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng