Barayi sun raka wata mata banki

Barayi sun raka wata mata banki

- An damke shugaban wasu yan fashi a jihar Ondo

- Sun raka wata mata banki domin ciro kudi N90,000

- Anyi garkuwa da yaranta ne a lokacin da ake raka ta

Barayi sun raka wata mata banki

Jami’an yan sandan jihar Ondo sun damke shugaban wasu barayi a jihar su ta Ondo.

An damke shi yayinda shi da abokan aikinsa suka yi garkuwa da yaran wata mata mai suna Folashade Jayeoba, kuma suka rakata banki domin ciro kudiN90,000.

Game da cewar jaridan Vanguard sun kwace katin ATM dinta ne kuma suka bita banki saboda babu kudi a gida yayinda ake rike da yaranta a matsayin garkuwa.

KU KARANTA: Yadda raba dai-dai zai lalata Najeriya – Murray-Bruce

Yayinda aka kama su , kwamishanan yan sandan jihar, Hilda Harrison, yace barayin sun je gidan matan ne sukayi mata fashi harda babban talabijin dinta.

Kwamishanan yace sunyi garkuwa da yaranta kuma suka bita bankin Keystone  da ke Akure, inda suka tilasta ta ciro kudi N90,000 a matsayin fansan yaran.

Shugaban gungun yan fashin, Samuel Ayodele ya shiga hannu kuma yana ofishin yan snadan Oke-Aro. An dame sauran aboan aikinshi a gidansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng