Hausawa da Yarbawa da Ibo sun hada

Hausawa da Yarbawa da Ibo sun hada

Hausawa, Yarbawa da Ibo gaba daya zasu hadu a biki na 25 na Oga Ikorodu Festival wanda za'a yi a mako mai zuwa.

Wadanda suka shirya bikin na gargajiya a Ikorodu a tsakiyar birnin Lagos, Ibo da ke yankin da Hausawa mazauna yankin, sun nuna ra'ayin su na ganin cewa bikin da za'ayi mai zuwa zefi sauran na baya haduwa, burgewa da kayatar wa.

Hausawa da Yarbawa da Ibo sun hada

A yar zantawar da manema labarai suka yi a Legas dan samun hasken abubuwan da zasu faru a bikin da za'ayi na kusan mako 1, Otunba Adekunla O. Oyebola, shugaban kungiyar Ikorodu Oga (IKODASS), yace masu shirya bikin suna kokarin ganin cewa bikin ya zama wanda aka fi halarta dan bude ido daga ko ina a fadin duniya.

Mun dauki babban mataki na yima kowacce ma'aikatar al'adu rejista, kuma muna kokarin ganin cewa bikin ya zama 1 daga cikin manyan bukukuwa da akayi a birnin Legas da kuma sauran jahohi har ma da duniya baki daya.

Dalilin yin wannan bikin dan ta watsu a duniya, kuma ta samu goyon baya kuma ta samu abunda ya dace da ita saboda kayatacce ne da gargajiyan ce kamar irin wadanda muka halatta a wasu kasashen.

Ya kara da cewa" Yarbawa da Hausawa yan arewa sun saka kansu sosai a wannan bikin, dan wannan ya nuna yadda mutanen Ikorodu suka dauki bikin da mahimmanci.

Wasu abubuwan da zasu faru a gurin sun hada da takarar wadda tafi kyau a gargajiyan ce, Worro cultural carnival da bikin tunawa da masu zane da Ikorodu Heroine cikin abubuwan da za'ayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel