Ba fa Najeriya kadai ke cikin matsin tattalin arziki ba- Buhari

Ba fa Najeriya kadai ke cikin matsin tattalin arziki ba- Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari bai gushe ba yana jaddada cewa ba waifa Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki ba

- Shugaban kasan yace wasu kasashn na cikin halin da yafi na Najeriya tsanani

- Amma, ya nanata cewa gwamnati na iyakan kokarinta wajen samar da mafita daga cikin matsalolin tattalin arziki

Ba fa Najeriya kadai ke cikin matsin tattalin arziki ba- Buhari
President Buhari

Kuma dai, shugaba Muhammadu Buhari ya kara Magana akan abin da ya shafi tattalin arzikin Najeriya yayinda yake Magana da daliban makarantan manufofi da ilimin dabaru watau National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPPS).

Sun gana ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranan Alhamis,3 ga Nuwamba.

KU KARANTA: Kalli yadda fafatawa tsakanin yan Boko Haram da Sojoji ta kasance

Shugaba Buhari yace: A shekara daya da rabin wannan gwamnati, tattalin arzikin ta fuskanci kalubale,musamman fadin farashin kudin man fetur, wanda ya shafi jama’an Najeriya talakawa.

Yanada muhimmanci ku san cewa ba wannan gwamnatin ta samar da wannan matsin tattalin arzikin ba amma rashin tattalin shekarun da suka gabata. Kuma ba Najeriya kadai ke cikin wannan hali ba, wasu ma nasu yafi haka tsanani.

Shugaba Buhari ya sake sukan gwamnatin baya, harda na Goodluck Jonathan akan almubazzarancin da sukayi wanda ya bada sakamakon matsin tattalin arziki.

Hakazlika, shugaba Buhari yayi kira gay an Najeriya cewa suyi hakuri da wannan gwamnati saboda tana cikin kokarinta na fitar da Najeriya dga cikin wanna hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng