Kwamitin ladabtarwa ta APC tace a kori Timi Frank
- Kwamitin ladabtarwa ta jam’iyyar APC ta rubuta wata kara akan mataimakin kakakin jam’iyyar , Timi Frank
- Rashin amsa gayyatar da akay masa, kwamitin ta bada shawaran cewa a dakatad da shi
Timi Frank ya kasance yana kiraga shugaban jam’iyyar APC, Chief John Oyegunn yayi murabus daga kujeransa saboda rashin iya shugabanci.
Wata kwamitin ladabtarwa da jam’iyyar APC ta nada domin gudananr da bincike cikin al’amuran mataimakin kakakin jam’iyyar, Timi Frank, ta bayar da shawaran cewa a dakatad dashi kuma a kore sa daga baya.
KU KARANTA: Ashe da gaske tusa na hura wuta?
Kwamitin ta gudanar da bincike akan Frank bisa ga wata kara da wani mamban jam’iyyar na jihar Akwa Ibom, Mr Aniekan Akpabio, wanda yace Frank yana bata sunan jam’iyyar a kafafan yada labarai, Vanguard ta bada rahoto.
Kwamitin wacce ta kunshi mutane biyar karkashin jagorancin Solomon Edoja domin bincike cikin karar. Amma Timi Frank yace ba zai amsa gayyatar kwamitin ba.
Ya tuhumci cewa shugaban jam’iyyar Oyegun ne ya nada kwamitin saboda a kore domin ya fallasa abubuwan mara kyau da ke faruwa a APC.
Kwamitin ya sallama rahoton ta a ranan Alhamis,3 ga watan nuwamba. Bisa ga rashin amsa gayyatar, kwamitin tace kawai a dakatad dashi kana kuma shugabannin jam’iiyar su Koreshi daga jam’iyyar.
Asali: Legit.ng