Abun mamaki, yan biyun da aka haifesu a kenya an raba su
Babu dadi ko kadan idan mutum ya haifi yaransa suka kasance suna da wani nakasa.
Yan biyun da aka haifesu kenan masu suna Blessing da kuma Favour wanda aka haifa a garin Kenya, inda aka bayyana cewar sun hadu ne wajen kashin su na baya.
Godiya ga jaruman likitocin da sukai yima yaran aiki, wanda akace sun kai su sittin. Amman saidai likitocin sun kafa tarihi akan samun wannan nasaran.
Likitocin a babban asibiti na Kenyata wato (KNH) wanda suka gudanar da aikin. Andai bayyana cewar sune likitoci na farko da suka samu nasaran yin irin wannan aiki a nahiyar Afirika, na samun nasaran raba yara biyu a hade.
Shidai aikin sunanshi aikin Sarcophagus, wanda ya kashe awa 23 anayin sa, daga ranar Talata da karfe 6 na safe zuwa ranar Laraba karfe 5 na safe.
Wa'anda suka taimaka wajen samun nasarar yima yaran aiki sun hada da kwararru a fannin Paediatric da Surgeons da Neutrosuegeons da Plastic Constructive Surgeons da Anaesthetists da kuma kungiyar Nurse.
Andai bayyana wannan irin aikin shine na farko da akayishi a kasar Kenyan dama Afirika gaba daya.
Yan biyun da aka haifesu a watan Satumbar shekarar 2014, yanzu haka suna shashin kula da lafiyar su a asibiti, inda akesa ran zasu samu lafiya nan bada dadewa ba.
Asali: Legit.ng