Hotunan kyawawan Igbo na aure
1 - tsawon mintuna
Hotunan kyawawan Igbo na aure ya watsu a shafin dandalin sadarwa na Instagram saboda haduwar da suka yi.
Femi Ogunbanwo na gidan hoton "marry me" ya saka hoton auren wadan nan kyawawan inyamurai wanda ya watsu a yanar gizo.
Ya dauke su a kayan su masu nuna al'adun cikakken inyamuri, wanda hoton ya saka masu amfani da shafukan Instagram magana.
Gashi macen an tace shi ya kalli sama inda akayi mai ado da jajayen murjani na ado irin na suku, duk sun rike abun nuna al'adun mulkin inyamurai mai gashi na gargajiya "wutsiyar doki". Kalli sauran hotunan.
Asali: Legit.ng