Wata mata yar kenya ta bayyana yadda ta kama mijinta yana

Wata mata yar kenya ta bayyana yadda ta kama mijinta yana

Matar mai suna Grace Maina, ta bayyana labarin yadda mijin ta dasuka kwashe shekaru shida suna tare ta sadu da ita.

Wata mata yar kenya ta bayyana yadda ta kama mijinta yana

Grace Maina, dai ta bayyana yadda tazo ta kama mijinta yana badala da yarinyar yar uwarta a gadonsu da suke kwanciya akai.

A yarda aka tura a shafin Kenya, an dai bayyana cewar matar ta kama mijin nata ne a kan gadonsu da suke kwanciya yana aikata badala da yarinyar yar uwar ta.

A inda nan da nan ta sakeshi bayan data tabbatar da yarinyar tanada ciki har na tsawon wata hudu na mijin nata. A inda ta rabu da mijin nata bayan wata daya da faruwar al'amarin. Su kuma sukayi aure daga baya. Gadai karin bayanin nata.

Ni sunana Grace Maina, ni mahaifiyar yara uku ce wanda a yanzu banda aure, nayi aure na tsawon shekaru shida. Mijina malamin makaranta ne, nikuma inada shagon saida kayan sawa a garin Nanyuki.

Muna tare dashi, bayan wani lokaci sai ya fara kwanciya da yan aikin da mukeyi a gidan. Haka dai yaci gaba, wata rana naje aiki to akwai yarinyar babban yayanmu tazo hutu gidan. Saina barta ita da kananan yara domin suyi aiki, kawai sai naji bacci nakeji saina yanke shawaran dawowa gida da misalin karfe 10 na safe.

Koda na dawo saina iske mijina akan yarinyar yayata yana aika badala da ita kuma akan gadona. Ko kunsan cewar na kallesu sosai kafin susan ina kallon su. Koda ya ganni sai yace mani wai nayi hakuri aikin shedan ne. Shine nace yarinyar tabar mani gidana kawai.

Sai na kira mama tace mani na dawo gida , yaran nawa. Koda mukayi bincike sai muka gane ashema tanada cikin shi na tsawon wata hudu. Ganin bazan iya jure ganin wannan abin kunyan ba, kawai saina saida shagona nabar garin. Yan shekara bakwai kenan da faruwar al'amarin, Bayan wata guda sai kawai ya auri yarinyar yayantawa, ni kuma na wuce da yarana, yanzu kuma yanata rokona na dawo nida yarana.

Allah ya sauwake! Me zaku iya cewa game da wannan abun?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng