Fastonmu yayi lalata da ni - Yvonne Smith
Wata budurwa ta tona asirin wani fasto wanda ya tilasta ta yayi lalata da ita da sunan karama.
Matar yar kasan South Afrika mai suna Yvonne Smith, ta tuhumci fasto Bongani Manyisa da yin lalata da ita bayan yayi mata addu’a.
Matar ta je wajen faston ne saboda tana neman taimako akan ciwon bugun jini amma sai da ta biya shi kudi N453,000 da kuma kwanciya da ita. Game da cewar ta, yace za’ayi watanni ana addu’an amma ya kasance yana lalata da ita da sunan nema mata lafiya.
KU KARANTA: Kuyi hattara da Sojoji: Kungiyar fafutuka ga Tsageru
Smith tace ta yanke shawaran tona masa asiri ne daga baya. Kuma ta fadawa shugabannin cocin kuma an kore shi.
Ga abinda tace: “Na kasance inada ciwon gudun jinni tun agustan da ya gabata. Ina zuwa asibiti amma babu wani canji. Sai aka gayyace ni coci inda faston ya mini addu’a. bayan na samu sauki, sai faston ya fara lalata da ni har nace na gaji.”
Asali: Legit.ng