Abubuwan kunyan da fastocin addinin kirista keyi a Najeriya domin neman duniya
- Mafi akasarin fastoci suna yaudarar jama’arsu ta hanyar sihiri da zamba
- Kuma idan aka kamasu ,sai su ce shaidan ne ya tura su,alhalin bokaye ne
Karanta Abubuwan da fasocin Najeriya keyi domin neman duniya
Shin menene fasto zai dinga yi da naman mutum. An kama wani fasto da naman mutum a watan mayu wannan shekaran. Faston cocin Living Faith Church a.k.a Winners Chapel mai suna Pastor Adeniyi Johnson.
A watan yuli, an damke wani faston cocin Anchor of Restoration Church mai suna Prophet Obi O. a jihar Delta, zindir haihuwar uwarsa da matar aure. Jama’an unguwan sun ko bashi kunya.
KU KARANTA:EU zata kashe N50 biliyan wajen bangaren wuta a Najeriya
A ranan 4 ga watan afrilu, an damke wani faston cocin Christ Apostolic Church (CAC), Agbala Dagunduro a jihar Ondo mai suna Moses Abiodun yayinda aka ga wasu abun ban tsoro a cikin cocinsa. An gay a birne kan saniya da kunkuru.
An damke wani faston cocin Day Spring Family Chapel, Egbeda area, Ibadan, mai suna Pastor Isaiah Ojo, inda yake fyade wata yar shekara 7.
Game da rahoto, an damke wani fasto Paul Morah yana luwadi da kananan yara 24 a jihar Ebonyi. Yana amfani da asiri wajen sihirce su.
Wani fasto mai suna Emmanuel Adeyemi, ya sanya ma yara 28 mari kuma ya boye su a cikin gidansa kafin yan sanda suka zo suka damke shi.
Asali: Legit.ng