Gareth Bale ya kafa wani tarihi a gasar Champions Lig

Gareth Bale ya kafa wani tarihi a gasar Champions Lig

-Gareth Bale ya zura kwallo mafi sauri a wasar da kungiyar shi Real Madrid ta doka da Warsaw Legia a tarihin Champions Lig                                             

- Kungiyar Real Madrid tayi kunnen doki a kayatacciyar wasar da suka doka 3-3 da Warsaw                                         

- Madrid suna cin 3-2 har kusan mintuna 87 na wasar sai Mateo Kovacic ya farke wasar

Kwallon da Gareth Bale ya zura a sekon 57 a wasar da Madrid ta doka da Warsaw itace kwallo mafi sauri a tarihin Champions Lig.

Real Madrid sun taba kwallo sau 27 kawai har da tabawar da Legia suka yi sau 1, ya bashi damar zura wasar bayan kwallo da Ronaldo ya taba da kai.

Gareth Bale ya kafa wani tarihi a gasar Champions Lig
Gareth Bale

Kwallon da ya zura abun mamaki ce, wadda yayi amfani da kafar hagu, daga wajen gurin finariti ya jefa ta raga.

Kwallon ta kasance lokaci na farko da Bale ya zura kwallo a wasa 2 a jere a gasar Champions Lig tun watan Nuwamba 2013, tunda ya jefa kwallo a wasar farko da suka yi 19 ga watan Oktoba.

Daga baya kuma Bale ya taimaka Benzema ya zura na shi, dan kasar Welsh din yana da kwallo 14 a wasa 43 da ya doka ta Champions Lig.

Real Madrid ta yi kunnen doki 3-3 da Legia a wasar, inda suka bar kungiyar Zidane da suna bin kungiyar Burrusia Dortmond a rukuni na F.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng