Mutane 4 sun rasa rayuka a rikicin yan kungiyar asiri
Kimanin mutane hudu aka kashe a ranar 2 ga watan Nuwamba yayin rikici ya balle tsakanin wasu kungiyoyin asiri a garin Ilorin a jihar Kwara.
Jaridar Leadership ta ruwaito rikicin ya fara ne a ranar Litinin 31 ga watan Oktoba a unguwar Gaa-Akanbi cikin birnin Ilori yayin da wasu kungiyoyin asiri dake gaba suka afka ma juna, inda aka kashe wani matashi mai shekaru 20.
Majiyar mu tace rikicin ya isa har zuwa yankin kasuwar Ipata da unguwar Kankatu a ranar Talata 1 ga watan Nuwamba inda aka kashe mutane biyu. Kisan ya faru ne da misalin karfe 4 na yamma da karfe 9 na yamma a kusa da gadar Amule na unguwar Kankatu.
KU KARANTA: Buratai ya baiwa daliban jihar Nasarawa 150 gurbi a NDA
Hakazalika wasu gungun matsafa sun kashe wani mutum dake kan hanyarsa ta zuwa aiki a ranar Laraba a unguwar Odota da misalin karfe 10 a safe.
Kaakakin rundunar yansandan jihar Kwara Ajayi Okasanmi ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma yace sun fara gudanar da bincike game da kashe kashen.
A wani labarin kuma, yansanda sun hallaka wasu yan fashi su biyu yayin wani artabu da sukayi a a jihar Delta. Wadanda aka kashe tare da abokinsu daya sha da harbin bindiga a jikinsa sun yi ma wani mutumi fashin kudi da wayoyinsa da misalin karfe 2pm na ranar Talata 1 ga watan Nuwamba.
&index=61&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt
Asali: Legit.ng