Bikin cikar Sarkin musulmi shekaru 10 a karagar mulki

Bikin cikar Sarkin musulmi shekaru 10 a karagar mulki

A yau 2 ga watan Nuwamba mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya cika shekaru 10 akan karagar mulki.

Mai alfarma Sa’ad Abubakar shi ne sarki na 20 a jerin sarakan musulunci tun bayan shehu dan Fodio. A watan Nuwambar 2016 ne aka nada shi Sarki don maye gurbin yayansa mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Maccido daya rasu a hadarin jirgi a filin tashin jirgi dake garin Abuja.

Bikin cikar Sarkin musulmi shekaru 10 a karagar mulki
Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar

Mai alfarma ya kasance wata hanyar kulla alaka tsakanin Musulmai da wadanda ba musulmai ba saboda kaunar sa na ganin zaman lafiya ya dawwama a kasar nan. yayin da yake yaba mai alfarma, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yace “zancen kokarin hadin kan kasar nan da zamanta cikin lafiya ba zai taba kammaluwa ba tare da an ambaci sunan mai alfarma sarkin musulmi ba. “Sultan mutum ne daya dage wajen yada zancen zama lafiya a tsakanin mu, tare da yin duk mai yiwuwa don hada kan al’umomin kasar nan”

Shi ma Kaakakin majalisar wakilai ba’a barsa a baya ba wajen yabawa ma Sultan, yace “Sultan a matsayinsa na shugaban gargajiya, yayi kokarin kawo kyakyakyawan zamantakewa tsakanin addinan kasar nan daban daban, tare da kawo zaman lafiya a kasa”

KU KARANTA:Kasar Zambia ta jaddada matsayin Najeriya a Afirka

A shekarar 2012 ne jaridar Leadership ta karrama Sultan da lamabar yabo ta gwarzon shekara tare da shugaban kungiyar addinin kirista ta Katolika John Onaiyekan. Sa’annan sunan Sultan ya sha shiga jerin mutane musulmai da suka fi shahara a duniya gaba daya.

Ga kada daga cikin mukamen da mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ke rike dasu:

Allah ya ja zamanin Sarkin musulmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng