Mai magana da yawun tsohon shugaba ya bayyana abun

Mai magana da yawun tsohon shugaba ya bayyana abun

- Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Reuben Abati ya ce ze dawo da miliyan N5 cikin miliyan N50m da ake zargin ya karba a hannun Dasuki                                       

- Abati yace duk kudin da ya karba yana da sauran miliyan N5 kawai                       

- Mai magana da yawun bakin tsohon shugaban kasa har yanzu yana hannun hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC

Mai magana da yawun bakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana shirye da ya dawo da miliyan N5 ga hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC.

Mai magana da yawun tsohon shugaba ya bayyana abun
Reuben Abati

Reuben Abati da har yanzu yana tsare a hannun hukumar EFCC a Abuja yace yana da miliyan N5m kawai cikin miliyan N5om da ake zargin ya karba a hannun tsohon mai bada shawara kan sha'anin tsaro, jaridar premium times suka ruwaito haka.

Abati yace ze biya kudin kasa da ya karba bayan yan kwanakin da yayi a rufe. EFCC sunce kudin da ya karba suna cikin kudin da Dasuki ya bannatar dan sayen makamai wadanda aka fi kira da DasukiGate.

DasukiGate dai ya samo asali daga sunan tsohon mai bada shawara kan sha'anin tsaro na kasa saboda raba kudaden kasa da yayi ga manyan kasar nan a lokacin yakin neman zaben jam'iyar PDP 2015.

Haka kuma Dasuki har yanzu yana tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya yana fuskantar shari'a a babbar kotun Abuja.

Sai dai  Abati wanda aka tsare tare da tsohon ministan sufurin jirage Fani-kayode tare da karamin ministan tsaro Musuliu Obanikoro jiya 31 ga watan Oktoba Fasto Mathew Kukah na Sokoto ya ziyarar ce su.

Lokacin ziyarar Faston yayi masu addu'a, kuma ya kara masu karfin guiwar suyi hakuri da wannan iftila'in da ya fada ma su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng