Biafra: Minista ya shawarci ga masu zanga zanga

Biafra: Minista ya shawarci ga masu zanga zanga

- Mninstan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya shawarci masu fafutukar neman Biafra da suyi aiki da abinda dokar Najeriga ta tanada

- Onyeama yace duk gungunan masu neman samun Biafra su kauce ma hargitsi domin nuna rashin jin dadinsu

- Ya kuma ce shugaba Muhammadu Buhari na aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin Najeriya Wanda ta gurgunce

Biafra: Minista ya shawarci ga masu zanga zanga

Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya bayar da shawara ga duk masu fafutukar neman kasar Biafra. Onyeama yayi magana a karshen mako a Jihar Enugu inda yace duk gungunan masu neman 'yancin Biafra dole ne subi kai'dojin kundin tsarin mulki da kuma hanyoyin diplomasiyya wajen neman bukatarsu.

KU KARANTA:Shugaba Buhari yaba da umurnin yin bincike akan zargin lalata da Yan gudun hijira

Ya kuma ce masu fafutukar har yanzu basu sami amincewar mutanen Igbo ba kamar yadda 'yan awaren Scotland suka sami amincewar wakilansu a majalisar Britaniya.

Ina mai ra'ayin cewa masu fafutukar ba da yawun Ndigbo suke magana ba kuma basu da amincewar kabilar Igbo suyi abinda suke yi. Shawara garesu itace su bi hanyar sasanci maimakon tashin hankali a ko da yaushe, cewar Onyeama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng