Jiragen ruwa 26 na kayan abinci na gab da sauka Najeriya

Jiragen ruwa 26 na kayan abinci na gab da sauka Najeriya

A yau 31 ga watan Nuwamba ne ake sa ran wasu manyan jiragen ruwa guda 26 dauke da kayan abinci, man fetur da sauran kayan masarufi zasu iso Najeriya ta tashoshin jiragen ruwa na Apapa, da na Tin-Can Island dake Legas.

Jiragen ruwa 26 na kayan abinci na gab da sauka Najeriya
Hadiza Bala Usman

Hukumar kula da tashohin jiragen ruwa dake karkashin jagorancin Hadiza Bala Usman ne ta bayyana haka a ciki rahoton ta mai suna ‘Shipping Position’.

Humar NPA tace jiragen da ake tsammanin shigowarsu na dauke da garin plawa, Sikari, man jirgin sama, gas, man fetur, da sauran kayayyaki. Bugu da kari wasu jirage hudu dake dauke da taki, Sikaru da mai sun sauka  a tashar jirgin ruwan.  A yanzu haka kuma akwai jirage 15 dake sauke kayayyakin da suka dauko.

KU KARANTA:Tsagerun Neja Delta sun fasa butututn mai a jihar Delta

Da yake tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne ga kayayyakin da ake shigowa dasu, hakan ne ya sanya tashoshin jirgin ruwa dake Legas suka fi kowane tashar jirgin ruwa hada hada a Afirka. Kusan duk sati sai wani jirgi ya sauka, wanda sakamakon haka ke sanyawa ba’a siyan kayayyakin da ake hadawa a gida Najeriya saboda arhar wadanda ake shigowa dasu.

A wani labarin kuma, hukumar tarayyar Turai da gwamnati Najeriya sun fara tattauna yiwuwar maido da yan Najeriya bakin haure da suka makale a kasashe Turai gida. Tattaunawar wani hanya ce da tarayyar Turai ta fito da shi don dakatar da yawan shigowar bakin haure yankinta ta cikin ruwa.

&list=PL6sEiOi0w1ZCJ2pYczvQeEWNY5u811xJt&index=5

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng