Mutum 1 ya mutu sanadiyar zanga-zanga a Ondo

Mutum 1 ya mutu sanadiyar zanga-zanga a Ondo

- Anyi zanga-zanga a karshen mako a jihar ondo sakamakon canjin sunan dan takaran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP da INEC tayi

- Wani dan sakansare ya rasa rayuwarsa a zanga-zanga yayinda yan sanda suka harbe shi da barkonon tsohuwa

Mutum 1 ya mutu sanadiyar zanga-zanga a Ondo

Zanga-zangan da akeyi a jihar Ondo sakamakon sauyin dan takaran da Hukumar INEC tayi ta zama doguwa, yayinda wani yaro dan makarantan sakandare ya rasa rayuwarsa a zanga-zangar.

Duk da cewa ba'a bayyana sunan yaton ba, an cigaba da zanga-zangar a Akure, yayinda matasa suka tsare tituna suna kona tayoyi.

KU KARANTA:Boko Haram sun farma sojin Operation Lafiya Dole, ku karanta aninda ya faru bayan haka

Hukumar INEC ta sauya sunan Eyitayo Jegede da Jimoh Ibrahim bisa ga umurnin Jastis Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kana, sarkin gargajiyan Akure, Deji of Akure, Oba Aladetoyinbo Aladelusi,yayi kira ga shugaba buhari da ya sa baki akan abinda Hukumar INEC tayi.

Deji of Akure, Oba Aladetoyinbo Aladelusi,ya bayyana hakan ne yayinda wasu yan jam'iyyar suka kawo masa kuka fadar sa da ke Akure. Yayi iira da bangaren shari'a ta sa baki, kuma su tabbatar da cewa babu zalunci a jihar ondo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng