Alkalai : EFCC tana bincikar manyan lauyoyi 3 akan cin hanci
- Hukumar EFCC ta gayyaci manyan lauyoyi akan cin hanci
- Ana tuhumar lauyoyin da turawa wasu Alkalai makudan kudi
- A yanzu dai, ana bincikan 3 daga cikin lauyoyin a ofishin EFCC da ke Legas a ranan 27 ga watan Oktoba
Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa hukumar EFCC tana bincikan lauyoyi 3 akan zargin rashawa. Sun amsa gayyatar EFCC a ranan alhamis 27 ga watan oktoba. Lauyoyin sune Paul Usoro, Gani Adetola-Kaseem, da Felix Fagbohungbe.
“Mun gano cewa rashawa a bangaren shari'a ta yi kamari," majiya tace.
KU KARANTA: Mai shari’a Abang ya zartar da hukunci kan zaben Ondo, ya kuma ci lawya tarar N100,000
Yayinda ana sauraron lauyoyi 20 zuwa 30 ,zasu zo suyi bayani akan rawan da suka taka wajen tura kudi.
“Wasu manyan lauyoyi da suka taimakawa wannan hukuma a wasu abubuwa ma na ciki. Gaskiya muna cikin matsala.”
Kana, harda lauyan Ali modu sherrif Niyi Akintola na cikin lauyoyin da aka gayyata, duk da dai har yanzu bai zo ba.
Ance yayi tafiya zuwa Abuja domin kare wani alkali a gaban Majalisar shari'a ta kasa akan wata kara.
“Duk alkalin da yaki amsa gayyata, EFCC zata yi amfani da doka wajen tabbatar da bin dokar kasa. Mun girmama dukkan lauyoyinda da suka amsa gayyata, bisa ga yadda yan kasar waje keyi.”
An tattaro cewa an gayyaci lauyoyin ne saboda ayi rufa-rufa saboda lauyoyin na taimakawa Hukumar.
Asali: Legit.ng