Yan sanda jihar Ogun sun kama yan kungiyar asiri
- Yan sanda sun kama yan kungiyar asiri a jahar Ogun
- Yan sandar shiya ta 2 na Onkan Koman na jahar Ogun sun gano maboyar yan kungiyar asiri
- Yan kungiyar asirin da aka kama an gurfanar da su a kotu
Abun ban al'ajabi, sashen tsaro na yan sanda na shiya ta 2 Onikam Legad Koman sun gano maboyar yan kungiyar asiri a jahar Ogun.
An gano gurin ne a Abule Ifa, unguwar Siun, ta karamar hukumar Obafemi Awode jahar Ogun, shugabanin tsafin guda 2 yan sanda sun kama su, an samu layoyi kayan tsafi a gurin su.
Mataimakin shugaban yan sanda na kasa na shiyar, Abdulmajid Ali shi ya jagoran ci manyan yan sanda dan, wanda ya hada da komishi nan yan sanda na jahar Ahmad Ilyas, sai OC na yankin DCP Suleman Balarabe, Komandan ZIS CSP Gbenga Megbope, da dai sauran su zuwa maboyar.
Dalilin tafiyar shine a gano gurin boyon na su, kuma a samu hanyar mai tsari da za'a ture ginin. Kamar yadda mataimakin shugaban yan sanda yace, gurin boyon yana da hadari, kuma gane su da akayi shi ya bamu damar kama wasu.
Kamar yadda Vanguard ta bayyana, yan damfara suna amfani da wurin da yan kungiyar asiri dan damfarar mutane da yin abubuwa na zalunci.
AIG yace a tisayan wanda akaje neman mabannata da yan ta'dda, sun samu sa'ar kama mutane 2 manyan kungiyar wadanda aka bayyana 1 a matsayin Taiwo Adeleke dan shekara 47, sai Kayode Oseni dan shekara 52.
Kuma ya yaba ma yan sanda kan namijn kokarin da suka yi, kuma yace suna shirye da su kawo karshen yin laifi, da masu aikata shi.
Yace za'a dauki kwararan matakai kan lamarin, kuma a gano yadda za'ayi aga an kai karshen wannan lamarin.
Ya kammala da cewa a yanzu haka an gurfanar da wadanda a ke zargi a kotu.
Asali: Legit.ng