Cece kuce tsakanin fulani makiyaya da gwamnatin jihar Ekiti

Cece kuce tsakanin fulani makiyaya da gwamnatin jihar Ekiti

- Kungiyar makiyaya ta Miyatti Allah a Najeriya ta koka akan matakin da tace gwamnatin jihar Ekiti ta dauka na haramtawa makiyaya kiwo a fadin jihar

- Taron manema labarai kungiyar Miyatti Allah ta kira a Minna ta jihar Neja, domin mayar da martani akan wannan mataki akan matakin na gwamnatin jihar Ekiti, mataimakin shugaban kungiyar Alhaji Husaini Boso, yace gwamnan jihar Ekiti ne da kansa idan yana tafiya a mota yaga Shanu yake tsayawa ya bayar da umarnin a harbi Shanun, hakan ta faru a gaban makiyaya

Cece kuce tsakanin fulani makiyaya da gwamnatin jihar Ekiti
Fulani makiyaya

Yanzu haka dai kungiyar ta dauki matakin rubutawa duk hukumomin da suke da hakki domin ganin an dauki matakin da ya kamata a cewar mataimakin shugaban kungiyar ta kasa.

Majiyar mu ta yi kokarin jin ta bakin gwamnan jihar Ekiti, amma yaci tura. Sai dai bayanai sun nuna cewa wata sabuwar doka ce gwamnatin jihar ta samar domin takaita makiyaya kiwo a jihar, domin kawo karshen barnar da gwamnatin jihar tace makiyayan na haddasawa.

Masanin Shari’a a Najeriya, Barista Dan Lami Wushishi, yace bai kamata ba ace gwamnan jiha da kansa yana fitowa kan titi yana aikata hakan, domin zai yana baiwa ‘yan zauna gari banza ‘yancin fitowa suna farma Shanun mutane. A cewar Barista babu wata dokar kasa da ta tanadarwa gwamnan yin hakan.

https://youtu.be/nT0m4FpgP-w

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: